SHARHIN LITTAFIN (MUHIMMAN DARUSSA GA DAUKACIN AL'UMMAH): Littafi ne da harshen HAUSA wanda Dr. Haisam Sarhaan ya tanade shi, domin sharha ga littafin AD-DURUSUL MUHIMMA LI AMATIL UMMAH, na Imam Ibnu-Baaz -Allah ya yi rahama a gare shi-, Mawallafin (Shaikh Haisam) ya tattara nau'ukan ilmomin shari'a a cikin littafin, musamman wadanda suka ta'allaka da hukunce-hukuncen fikihu, da akida, da halayya, wadanda ya dace ga daukacin al'ummah su sansu. Kuma Mawallafin ya sanya littafin cikin wani tsari mai kyau, ta fiskar sanya shi cikin jadwala, da rarraba shi daki-daki, Kuma ya ambaci muhimman manufofin addini, da dunkulallun ma'anoni, Kuma a bayan kammala kowane yanki na littafin, Mawallafin ya tsara tambayoyi da jarrabawan da suka ta'allaka da wannan babin, Kuma ya ambaci dukkan wadannan ne; ba tare da takaicewar da zata cire wasu fa'idodi ba, ko tsawaitawa mai gajiyarwa mai sanya kosawa.
wagga madda an tarjamata zuwa
- português - Portuguese
- اردو - Urdu
- Deutsch - German
- Shqip - Albanian
- español - Spanish
- বাংলা - Bengali
- bosanski - Bosnian
- ไทย - Thai
- हिन्दी - Hindi
- فارسی - Persian
- Türkçe - Turkish
- 中文 - Chinese
- Bahasa Indonesia - Indonesian
- Wikang Tagalog - Tagalog
- Français - French
- English - English
- አማርኛ - Amharic
- Русский - Russian
- العربية - Arabic
- नेपाली - Nepali